Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-29 14:13:21    
Ra'ayin "'yan mulkin mallaka na kasar Sin" ba shi da tushe ko kadan

cri

Tun shekaru 30 da suka wuce na bayan kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasar Sin da Kamaru, dangantakar da ke tsakanin kasashen 2 ta samu bunkasuwa lami lafiya, hadin gwiwar da ake yi tsakanin su domin samun moriyar juna shi ma yana ta samun ci gaba a kowace rana. Yanzu 'yan kasuwa na kasar Sin sai kara yawa suke suna ta zuwan kasar Kamaru. Mr. Essama Essomba ya yi jinjina a kan wannan cewa, "Hajjojin kasar Sin suna da kyau, farashinsu kuma ya yi araha. 'Yan kasuwa na kasar Sin suna yin kasuwanci cikin sahihanci, kayayyakin kasar Sin kuma suna da inganci."

Mr. Essama Essomba ya bayyana tabbas cewa, kasar Kamaru tana maraba da zuwan masu masana'antu matsakaita da kanana na kasar Sin don su zaba jari a nan kasar Kamaru. Idan an zuba jari kadan za a iya samu moriya nan da nan, fararen hula ma za su iya samu moriya da sauri. Ban da wannan kuma, Afirka ita ma tana fatan kasar Sin za ta kara nuna goyon baya da yawa wajen fasaha don taimaka wa Afirka ga tabbatar da samun bunkasuwa mai 'yanci kuma cikin dogon lokaci.

A lokacin da Mr. Essama Essomba ya tabo magana kan taron dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da za a yi a nan gaba kadan ya amince sosai cewa, "Wannan gagarumin taro zai kara sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin Afirka baki daya ciki har da Kamaru, ta yadda jama'ar Afirka za su iya tsomo fasahohin da kasar Sin ta samu wajen bunkasa tattalin arzikin kasar."


1  2  3