Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-29 14:13:21    
Ra'ayin "'yan mulkin mallaka na kasar Sin" ba shi da tushe ko kadan

cri

"Gudummawar da kasar Sin ta ba wa kasar Kamaru ta gwada misalin koyo ga hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin. Ban yi tsammani cewa wai gudummawar da kasar Sin ta bayar ko jarin da ta zuwa a nahiyar Afirka sun zama "sabon mulkin mallaka ne", Mr. Pierre Essama Essomba, shugaban majalisar kafofin watsa labaru na kasar Kamaru shi ne ya yi wannan magana kwanan baya domin jinjina gudummawar da kasar Sin ta ba wa Afirka. Ya bayyana tabbas cewa, irin zancen da aka yi na wai "kasar Sin tana yin sabon mulkin mallaka a Afirka" ya zama kyashi ne da tsirarrun kafofin watsa labaru na kasashen yamma ke yi wa kasar Sin".

Mr. Essama Essomba ya ba da misali cewa, kasar Sin ta ba da taimako ga kasar Kamaru wajen yin muhimman gine-gine da yawa ciki har da babban dakin majalisar dokokin kasar, da makarantu da asibitoci, kuma ta ba da taimako ga Tanzaniya da Mauritaniya wajen shimfida hanyar dogo da hanyoyin motoci. Ya ce, "Da akwai bambanci sosai a tsakanin gudummawar da kasar Sin ta ba wa Afirka da mulkin mallaka da 'yan mulkin mallaka na kasashen yamma ke yi wa Kamaru da sauran kasashen Afirka. 'Yan mulkin mallaka na kasashen yamma ba su ba wa Kamaru kome ba, amma Kasar Sin ta kawo mana moriya da gaske."


1  2  3