Mr. Essama Essomba ya ce, daga fannin hukumar kasa ana iya cewa, hadin gwiwar da ake yi tsakanin Kamaru da kasar Sin ya samu moriyar juna kuma an samu nasara tare, daga wajen jama'a kuma an ce, gudummawar da kasar Sin ta ba wa Kamaru ta samar da zaman jin daji ga fararen hula na kasar.
Lokacin da Mr. Essama Essomba ya tabo magana kan kungiyar masu aikin jiyya ta kasar Sin da ke Kamaru, ya ce, kungiyar masu aikin jiyya ta kasar Sin ta samu kwar jini sosai daga wajen mutane, tana da cikakken kayayyakin asibiti, kuma masu aikin jiyya na kungiyar sun kware sosai wajen sana'arsu, farashin magungunan da suke sayar ya dace yadda ya kamata, sabo da haka sun samu muraba daga wajen fararen hula sosai.
1 2 3
|