Madatsar ruwa ta Sanxia a kan Kogin Yangtse na kasar Sin aikin tsaren ruwa ne mafi girma a duniya. An fara yin aikin gina ta ne a watan Disamba na shekarar 1994, kuma tun bayan da aka kammala aikin gina ta a ran 20 ga watan Mayu na shekarar nan, an riga an yi aiki da madatsar ruwan nan a manyan fannoni uku, kamar tara ruwa da zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma ba da wutar lantarki.
Amma bayan da tsayin ruwa da ake tattarawa ya kai mita 156 a madatsar ruwa ta Sanxia a kan Kogin Yangtse na kasar Sin, za a gamu da kalubale mai tsanani a fannoni da dama. Da Malam Zhang Shuguang, shugaban ofishin kula da ayyuka na babban kamfanin gina madatsar ruwa ta Sanxia a kan Kogin Yangtse na kasar Sin ya tabo magana a kan kalubalen nan, sai ya ce, mun riga mun dauki matakai wajen magance wadannan kalubale, musamman kamar girgizar kasa da ambaliyar ruwa. Ya bayyana cewa,"mun riga mun binne wasu na'urori a karkashin kasa, yayin da muka gina madatsar ruwa ta Sanxia. Yanzu za mu iya amfani da wadannan na'urori wajen sanya ido ga halin da ake ciki dangane da madatsar ruwan nan. Alal misali, yayin da muke tattarawar ruwa a madatsar ruwa ta Sanxia a yanzu, mu ma muna amfani da na'urorin nan wajen sanya ido sosai ga girgizar kasa da mai yiwuwa za ta auku bisa sanadiyyar tara ruwan. Idan mun gano alamun aukuwar girgizar kasa, to, nan da nan za mu sanar da su ga hukumomi da abin ya shafa."
1 2 3
|