Ranar 20 ga wata da dare, an sake maido da aikin tara ruwa a madatsar ruwa ta Sanxia a kan Kogin Yangtse na kasar Sin. Zuwa tsakiyar watan gobe, tsayin ruwa na madatsar ruwan zai dagu daga mita 135 zuwa mita 156. Bayan kammala aikin tara ruwan, za a kara aiki da madatsar ruwa ta Sanxia bisa mataki na farko, wajen rigakafin ambaliyar ruwa da zirga-zirgar jiragen ruwa da ba da wutar lantarki da sauransu.
Malam Zhang Shuguang, shugaban ofishin kula da ayyuka na babban kamfanin gina madatsar ruwa ta Sanxia a kan Kogin Yangtse na kasar Sin ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, ana gudanar da aikin tattarawar ruwa a madatsar ruwa ta Sanxia kamar yadda ya kamata. Ya kuma ce, bayan da tsayin ruwa da ake tattarawa a madatsar ruwan nan ya kai mita 156, za a kara aiki da madatsar ruwan nan bisa mataki na farko, kafin shekara daya ta cika. Ya kara da cewa,
"tattarawar ruwa da tsayinsa ya kai mita 156 a madatsar ruwa ta Sanxia a kan Kogin Yangtse, yana da muhimmanci sosai ga aikin gina madatsar ruwan. Kuma ya alamanta cewa, za a kara aiki da madatsar ruwan wajen rigakafin ambaliyar ruwa da zirga-zirgar jiragen ruwa da ba da wutar lantarki. "
1 2 3
|