Wani nunin zane-zanen fenti na Feng Shaoxie da ake yi yanzu a gidan nunin zane-zane na kasar Sin wanda ke da lakabi haka: Zanen da aka yi kan kurciyar Gabas ta tsakiya ta jawo sha'awar rukunin masu yin zane-zane da 'yan kallo na kasar Sin. Wadannan zane-zanen fenti da aka yi nuninsu tare da jigon batun zaman lafiya a Gabas ta tsakiya su ne zane-zane kadan da aka yi a tarihin zane-zanen kasar Sin wadanda a cikinsu aka mai da hankali sosai ga manyan al'amuran kasa da kasa, kuma sun bayyana cewa, muryar zuciyar Feng Shaoxie ta kira zaman lafiya ta hanyar yin amfani da alkalamin zane-zane ta yi daya da ta sauran mutane.
Nunin nan yana kunshe da manyan zane-zane 18 da ke da tsawon mita 2.5 tare da fadin mita 2 kowanensu. Shiga cikin dakin nune-nune ke da wuya, sai 'yan kallo suka nuna sha'awa sosai ga zanen da aka yi da ke da lakabi haka: Kurciyar zaman lafiya da ke Gabas ta Tsakiya. A cikin zanen, an bayyana cewa, kurciya mai launin fari da ta ji rauni ta zubar da jini a duk jikinta, tana nan tana cire bandaje da ke da jini . A cikin hayakin yaki , da akwai tutar mulkin kasar Isra'ila da ta Palesdinu a bayan kurciyar, wannan ya sa mutane suka shiga zulumi sosai. A cikin wani zane daban da ya yi da ke da lakabi haka: Wakar zaman lafiya. A cikin zanen, an kara girman takardar shirye-shiryen wake-wake da aka samu daga wajen aljihun coat na tsohon firayim ministan kasar Isra'ila Yitzhak Rabin, takardat ta jika da jini da yawa, wasu gasun kurciya da ke da jini suna tashi suna sauka, wannan ya alamanta mutuwar Mr Rabin wato kurciyar zaman lafiya. A cikin sauran zane-zanen da ya yi da akwai abubuwa dangane da radadin da marayyu na kasar Isra'ila da Palesdinu suke sha da kuma idannunsu da ya zana tamkar suke cikin zullumi. Sa'anan kuma da akwai zane-zane dangane da kyakkyawan matan da suka fasa boma bomai tare da jikinsu da waiwayen da tsohon firayim ministan kasar Isra'ila Sharon ya yi cikin halin tsanani da kuma Tsohon shugaban Palesdinu Yaser Arafat ya ba da lacca cikin fushi sosai da kuma keken guragu na shugaban kungiyar masu yin dagiya ta musulmin Palesdinu Sheikh Ahmed Ismail Yassin da kuma katangar da ke tsakanin kasar Isra'ila da Palesdinu a karkashin inuwar mukumuku sanyi da buda da dai sauransu.
1 2 3
|