An ce, har kullum, gwamnatin kasar Sin tana kara karfinta na yaki da ayyukan satar fasaha. Amma sabo da wasu kayayyakin ainihi da ke dauke da bayanai na sauti da hotuna suna da tsada gwargwadon copy dinsu na jabu, shi ya sa da kyar su sami karbuwa. Sabo da haka, jami'an gwamnati da dama suna son daukar matakai, don sassauta farashin kayayyakin ainihi, ta yadda za a cimma burin yaki da aikin satar fasaha. A halin yanzu dai, hukumar wallafe-wallafe ta birnin Shijiazhuang tana aiwatar da wani shiri na tallafa wa kayayyakin manhaja na ainihi. Yayin da yake hira da wakilinmu, mataimakin shugaban hukumar, Zhang Xiufang ya ce, 'Da ma mu kan yi bincike ne kawai. Amma bayan da muka kawo karshen binciken, ayyukan satar fasaha su kan sake samun farfadowa. Yanzu za mu bi asalin matsalar, za mu tattauna da shahararrun kamfanoni wadanda aka sanya su cikin jerin kamfanonin da gwamnati za ta ba su kwangila, don su sassauta farashin kayayyakin manhaja nasu. Wani muhimmin abu a wajen daidaita matsalar satar fasaha shi ne daidaita batun farashi mai tsada. Yanzu mun gayyaci wasu kamfanoni, mun cusa kayayyakinsu na manhaja cikin guda daya, kuma muna sayar da su da kudin Sin yuan 100, don daidaita wannan matsalar farashi mai tsada.' (Lubabatu) 1 2 3
|