Abin da kuke saurara yanzu shi ne binciken da kungiyar ke yi a wata kasuwar sai da kayayyakin da ke dauke da bayanai na sauti da hotuna da ke cibiyar birnin Shijiazhuang. Masu bincike sun gano cewa, faiyafan CD da wani kanti ke sayarwa, ba a buga tamburan SID sosai a kansu ba, shi ya sa mai yiwuwa ne suna da hannu cikin aikin satar fasaha. Wang Song, wani jami'in babbar hukumar kula da wallafe-wallafe ta kasar Sin wanda ke kula da binciken ya ce, 'dalilin da ya sa mun binciki wasu faiyafan CD a dazun nan, shi ne sabo da ba a iya ganin tamburan SID da aka buga a kansu sosai ba. Sabo da haka, mun kara binciken takardunsu na doka, kuma mun ga suna da cikakkun takardun doka. Shi ya sa da mu koma, za mu bincike me ya sa ba a iya ganin tambarinsu na SID sosai ba.'
Tun bayan da aka fara aiwatar da aikin musamman na yaki da ayyukan satar fasaha, hukumomi da dama da ke kula da wallafe-wallafe da al'adu na lardin Hebei sun kara bincike a kasuwannin sai da kayayyakin da ke dauke da bayanai na sauti da hotuna da kuma manhaja.
1 2 3
|