Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-19 19:48:04    
Kamata ya yi a tallafa wa kayayyaki na ainihi a yayin da ake yaki da copy dinsu na jabu

cri

A halin yanzu dai, gwamnatin kasar Sin tana aiwatar da aikin yaki da ayyukan satar fasaha a duk fadin kasar Sin, don bincike yadda ake gudanar da aikin a wurare daban daban, kwanan baya, kungiyoyin sa ido na hadin gwiwar hukumomin gwamnati da dama, sun kai ziyarar sirri a lardunan Guangdong da Hubei da Shan'xi da Hebei da dai sauransu, sun kuma yi shawarwari da hukumomin wuraren. Wakilinmu ma ya bi wata kungiyar daga cikinsu zuwa birnin Shijiazhuang na lardin Hebei, don ya ga yadda ake aiwatar da wannan aiki na yaki da ayyukan satar fasaha.

Birnin Shijiazhuang yana da nisan kilomita 300 daga kudancin birnin Beijing. Sabo da kasancewarsa a mahadar hanyoyi, shi ya sa ya zama wani muhimmin wuri da ake bi don jigilar haramtattun kayayyaki, sabo da haka kuma, yana shan wahalar ayyukan satar fasaha. A sa'i daya kuma, yadda ake yaki da ayyukan satar fasaha a nan birnin yana kawo muhimmin tasiri kai tsaye kan biranen Beijing da Tianjin da dai sauran biranen da ke makwabtaka da shi. Kungiyar sa ido ta hadin gwiwa da ta nufi birnin nan na Shijiazhuang tana da wakilai daga babbar hukumar kula da wallafe-wallafe ta kasar Sin da hukumar kula da hakkin mallakar ilmi ta kasar Sin da ma'aikatar tsaron jama'a da dai sauran hukumomi.


1  2  3