Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-19 15:58:37    
Yin hira da mutanen da suka zama a gabobin tabkin Baiyangdian

cri

Ban da tsire-tsiren reed kawai ba, ba a iya manta da kallon furannin lotus a tabkin nan ba. Lambun furannin lotus wuri ne na musamman da hukumar wurin ta kebe don noman irin wadannan furanni. Lokacin zafi lokaci ne da furannin lotus suka yi toho. Wadannan furanni sun mamaye rabin ruwan da ke cikin wannan lambu, ganyayen furannin sun rufe ruwan. Furannin lotus su kan yi rawa a sakamakon iska. An shimfida wata hanya a cikin lambun, amma furannin lotus da ganyayensu sun rufe ta, shi ya sa a lokacin da masu yawon shakatawa suke tafiya a kanta, sai ka ce mutane suna tafiya a kan furannin. Madam Zhao Jie, wadda ta zo nan don kallon furannin lotus, ta ce,

'Ina jin dadi saboda ganin furannin lotus masu yawan haka, ban taba ganin da yawa daga cikinsu a da ba. Furannin suna da kyaun gani kwarai, na dauki hotuna da yawa zan nuna wa abokaina.'

Da can masunta na wurin sun ciyar da iyalansu ta hanyar kiwo da kama kifi, amma yanzu yawancin mazaunen wurin sun ci riba daga aikin yawon shakatawa, sun yi amfani da jiragen ruwansu wajen jigilar da masu yawon shakatawa a ko wace rana.

Ban da wannan kuma, idan masu yawon shakatawa suka kai wa tabkin Baiyangdian ziyara, dole ne su ci kifayen wurin. Kiyaye iri-iri da yawa suna zama a cikin tabkin nan, wadanda namansu ke da matukar dadin ci, kuma suke iya samar da abubuwa masu gina jiki. Masu yawon shakatawa sun iya zuwa tabkin tare da masuntan wurin, su kama kifaye da kansu, daga baya, su shiga cikin ko wane dakin cin abinci na wurin tare da kifayensu, kuku suna son dafa kifaye ga masu yawon shakatawa. Saboda haka, masu yawon shakatawa su kan ji dadi iri na musamman.(Tasallah)


1  2  3