Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-19 15:58:37    
Yin hira da mutanen da suka zama a gabobin tabkin Baiyangdian

cri

Tsire-tsiren reed da ke zama a ko ina a cikin tabkin Baiyangdian suna da amfani sosai. Mazaunen wurin su kan ce, darajar wani tsiren reed ta yi daidai da ta wata sandar zinare. A watan Agusta da na Satumba na ko wace shekara, tsire-tsiren reed da ke tabkin Baiyangdian sun nuna, launinsu ya zama rawaya kamar iri na zinare, ta haka dukan tabkin ya zama rawaya, suna da kyaun gani sosai.

An raba tsire-tsiren reed na tabkin Baiyangdian zuwa matsayi 3 bisa ingancinsu. Mazaunen wurin sun saka labule da tsire-tsiren reed na matsayi na farko, sun yi zane-zane da iri na matsayi na 2, sa'an nan kuma, sun samar da takardu da iri na matsayi na 3, ko kuma sun mayar da su kamar makamashi ne wajen samun wuta. An yi romo da kuma giya da danyun saiwoyin reed, tsoffin saiwoyinsu kuwa sun zama magani. An kera tsintsiyoyi da tsininnukan reed, an kuma cika matasai da catkin na reed. Madam Yang Xue ta tafiyar da wani kanti, inda ta sayar da kayayyakin tsire-tsiren reed da ta yi da hannu. Ta yi bayanin cewa, ba ma an iya tara kayayyakin da aka saka da reed, ko kuma mayar da su abubuwan tunawa kawai ba, har ma suna da amfani a fannoni da yawa. An iya sanya wata hular reed don kare rana, haka kuma an iya jin dadi a lokacin da ake yawo a tabkin Baiyangdian saboda sanya takalman reed. Ta ce,

'An saka takalma da tsire-tsiren reed, wadanda aka gyara su tukuna, shi ya sa idan wani mutum ya sanya takalman reed, kafofinsa bai ji zafi ko kadan ba. Kayayyakin da nake sayarwa a nan kayayyaki ne da mazaunen wurin suka saka da tsire-tsiren da ke zama a cikin ruwa, shi ya sa sun nuna halin musamman na tabkin Baiyangdian.'


1  2  3