
Kuna dai sauraron shirinu na yawon shakatawa a kasar Sin ne daga sashen Hausa na Rediyon kasar Sin. Yanzu za mu ja gorarku zuwa tabkin Baiyangdian da ke kusa da birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, inda za ku fahimci yadda zaman rayuwar mutane yake, wadanda ke zaune a kusa da ruwa.
Tabkin Baiyangdian yana cikin gundumar Anxin ta lardin Hebei na kasar Sin, wanda ke da nisan kilomita fiye da 160 a tsakaninsa da Beijing. Fadin ruwan wannan tabki ya kai murabba'in kilomita misalin 366, wanda ya hada da kananan tabkuna fiye da 140 gaba daya. Akwai wata almara game da dalilin da ya haddasa wadannan kananan tabkuna a nan. Madam Ren Li, wadda ke jagorancin yawon shakatawa, ta bayyana cewa,
'An ce, a wani daren da ke da cikakken farin wata, wata angel mai suna Chang E ta ci magani iri na musamman a asirce, ta tashi zuwa sararin sama, ta yi sakaci, madubin da ke cikin aljihunta ya fadi, an fasshe shi zuwa sassa 143, saboda haka an samu wadannan kananan tabkuna guda 143 a nan.'
1 2 3
|