Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-14 20:09:58    
Kogon Mogao

cri

Fasahar kogon dutse na Dunhuang fasaha ce da ta hade da fasahohin gine-gine da sassakakkun kayayyaki da zane-zane, bisa harsashin ci gadon kyawawan al'adun gargajiya na kabilar Han da ke yankin tsakiya na kasar Sin da na sauran kabilun da ke yammacin kasar, masu fasaha na zamanin da sun tsamo dabarun nuna fasaha na kasashen waje da yin amfani da su, kuma sun samu bunkasuwa ta yadda suka zama kayayyakin fasaha na addinin Budda.

Sassakakkun kayayyaki masu launi sun zama wani muhimmin kashi ne daga cikin fasahar Dunhuang, daga cikinsu har da mutum-mutumin Budda da na manyan limamai mabiyansu, ire-iren kayayyaki masu launi da aka sassaka suna da yawan gaske. Mutum-mutumi mafi tsayi ya kai mita 34.5, wanda mafi kankanta kuma ya kai sentimita 2 kawai, akan daukaka kogon Mogao da suna babban dakin ajiye sassakakkun kayayyaki masu launi na addinin Budda sabo da arzutattun kayayyakin tarihi da kwarewar yin su.

Bayan da aka binciki fasahar yin zane-zanen bangaye da yawa an gano cewa, bisa harsashin cin gadon al'adun al'ummar kasar Sin, masu fasaha na zamanin da kuma sun tsamo fasahar kasashen Iran da Indiya da Greece, wannan ya alamanta wayin kai na al'ummar kasar Sin sosai.

Halayen musamman da aka bayyana a dauloli daban-daban wajen yin zane-zanen bangaye sun nuna halin siyasa da tattalin arziki da al'adu na mulkin gargajiya na kasar Sin, wannan ya zama wani shafi mai haske na tarihin zane-zanen zamanin da na kasar, kuma ya gabatar da bayanai masu daraja domin binciken tarihin zamanin da na kasar Sin.

Bayyanuwar fasahar Dunhuang ta shahara a kasar Sin da kasashen waje, tana da muhimmiyar daraja a fannin ba da taimako ga yin binciken abubuwan tarihi na kasar Sin. (Umaru)


1  2  3