Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-14 20:09:58    
Kogon Mogao

cri

An fara sassaka mutum-mutumin da ke cikin kogon Mogao daga shekarar 366 ta lokacin daular Qin, kuma an gama aikin a shekarar 1368 ta daular Yuan, wato an shafe shekaru 1000 ana ta sassakawa, ta yadda kogon Mogao ya zama ma'adana mai daraja wajen fasahar addinin budda wadda ta ke hade da fasahar gine-gine da sassakakkun kayayyakin dutse da zane-zanen bangaye da yin mutum-mutumi masu launi, kuma ya zama ma'adana mai daraja ta fasahar addinin budda kuma mafi girman sikeli, mafi yawan kayayyakin tarihi kuma mafi dadadden tarihin duniya. Irin wadannan kayayyakin tarihi masu daraja wajen fasaha ba ma kawai sun bayyana addinai da zaman rayuwar mutane na tsohon zamanin kasar sin ba, hatta ma sun bayyana basirar da jama'a ma'aikata na dauloli daban-daban suka nuna da manyan nasarorin da suka samu wajen gine-gine.

An gano "kogon ajiye littattafan Buddanci" ba zato ba tsammani a shekarar 1900. A cikin kogon an ajiye kayayyakin tarihi da yawansu ya kai dubu 60 na dauloli daban-daban daga karni na 4 zuwa na 14. Wannan ya zama wata babbar nasara ce da aka samu a karni na 20 wajen binciken kayayyakin tarihi, wannan kuma ya girgiza duk duniya baki daya, daga bisani kuma an kyautata wannan ilmi har ya zama shahararren "ilmin Dunhuang". Bayan da aka shafe kusan shekaru 100 ana ta yin binciken ilmin Dunhung, ba ma kawai an sami sakamakon da ya jawo hankulan mutane a fannin ilmi da fasaha da al'adu ba, har ma kuma ya nuna wa duniya kyakkyawar fasaha ta Dunhuang, da arzutattun al'adun gargajiya, da hazikancin jama'a ma'aikata na kasar Sin ta zamanin da.

Kwamitin kula da kayayyakin tarihi na duniya ya daukaka cewa, kogon Mogao wani muhimmin tsare-tsare ne da ke kan hanyar siliki. Ba ma kawai ya zama tashar yin mu'amala tsakanin kasashen gabas da na yamma wajen yin ciniki ba, amma har kuma ya zama magamin addinai da al'adu da ilmi. Kogon Mogao yana da kananan koguna da dakunan ibada 492 wadanda suka shahara a duniya sabo da mutum mutumi da zane-zanen bangaye masu daraja da ke ciki, sun nuna fasahar addinain Budda wadda take da tarihi na shekaru 1000.

1  2  3