Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-14 20:09:58    
Kogon Mogao

cri

Kogon Mogao yana gabashin tudun Mingsha da ke birnin Dunhuang na lardin Gansu wanda akan kira "Kogon Budda dubu daya", wanda kuma shi ne ma'adana mai daraja ta fasahar addinin Budda kuma mafi babban sikeli na duniya. Kogon Mogao yana da bene 5 wadanda a wurin mafi tsayi har ya kai mita 50, wadanda kuma aka gina su ta tsararriyar hanya, tsawon kogon daga kudu zuwa arewa ya kai fiye da mita 1600. Daga cikin kogon Mogao akwai manya da kananan koguna 492, fadin zane-zanen da aka yi a bangayen koguna ya kai fiye da murabba'in mita dubu 45, yawan mutum-mutumi masu launi ya kai fiye da 3000, ban da wannan kuma da akwai manyan gine-gine 5 wadanda aka gina da katako a lokacin daular Tang da ta song. Kogon dutse na Mogao yana hade da fasahar gine-gine da ta zane-zane da ta sassakakkun kayayyaki sosai, shi ne ma'adana mai daraja ta fasahar kogon dutse inda aka ajiye kayayyakin tarihi mafi yawa na kasar Sin. A shekarar 1987, an shigar da shi cikin "Sunayen abubuwan al'adun gargajiya na tarihin duniya".

Kogon Mogao yana kan tudun Mingsha da ke kudu maso gabashin birnin Dunhuang da nisan misalin kilomita 25 na lardin Gansu da ke yammacin kasar Sin. A nan akan samu isasshen hasken rana a duk shekara, kuma busashen yanayi ne wato ba a samun ruwan sama da yawa. A nan kuma akan samu yanayi 4 a shekara wato bazara da lokacin zafi da kaka da kuma hunturu, da rana akwai zafi amma da dare akwai sanyi. Kogon Mogao yana da babban sikeli, kayayyakin tarihin da ake da su cikin kogon suna da yawan gaske, kuma suna da dadadden tarihi. Kogon Mogao da kogon Yungang da ke lardin Shanxi da kogon Longmen da ke lardin Henan sun zama "manyan ma'adana 3 masu daraja wajen fasahar kogunan duwatsu" na kasar Sin.

1  2  3