Zhenjie da Yanzi, garinsu daya ne wato birnin Chengdu na lardin Sichuan. Iyayansu sun kai su makarantan koyon fasahar buga kwallon tennis ne domin inganta lafiyar jikinsu. Zhenjie da Yanzi suna zaman tare kuma suna horon wasan tare tun suna da shekaru 7 da haihuwa. Saboda haka, kullum sukan yi hadin gwiwa sosai tsakaninsu a gun gasa.
An haifi 'yar wasa Yanzi ne a shekarar 1984. Kuma an kai ta kungiyar lardin Sichuan lokacin da take da shekaru 14 kawai da haihuwa; A shekarar 1999, an kai ta makarantar koyon wasan kwallon tennis ta Knicks a kasar Amurka. Kuma an shigar da ita cikin kungiyar kasa a shekarar 2001 bayan ta dawo gida. Tun daga wannan lokaci ne, ta fara yin hadin gwiwa tare da Zhenjie domin horon wasan kwallon tennis na tsakanin mata bibbiyu.
Bayan da suka samu lambar zinariya a budaddiyar gasa ta wasan kwallon tennis ta Wimbledon, sun furta, cewa ' Mun lallasa abokan karawarmu har mun zama lambawan a filin wasa na ciyayi wanda ba mu saba ba, lallai wannan ya kara aniyarmu a gasannin nan gaba'.
Ana sa ran alherin cewa, za su ci gaba da samun nasara a filin wasan kwallon tennis kuma za su samu lambar zinariya a taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008.(Sani Wang ) 1 2 3
|