Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-08 16:35:00    
'Zakaru Zhenjie da Yanzi a wasan kwallon tennis na tsakanin mata bibbiyu

cri

Ba a manta ba, a gasar karshe ta wasan kwallon tennis na tsakanin mata bibbiyu da aka yi a kasar Australiya a farkon wannan shekara, 'yan wasa Zhenjie da Yansi sun lallasa abokan karawarsu wato 'yan wasan kasashen Amurka da Australiya su Lisa Raymond da Samantha Stosur da ci biyu da daya duk da cewa sun sha kashi a karo na farko. Don haka, sun kafa tarihi har sun dauki kofin zakara na farko ga kasar Sin a cikin gagarumar gasa da aka gudanar.

Kuma ba a manta ba, gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da aka gudanar ta janyo hankulan masu sha'awar kwallo na kasar Sin. Amma duk da haka, ganin rawa da 'yan wasa su Zhenjie da Yanzi suka nuna a budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta Wimbledon ta shere dimbin mutanen kasar Sin, wadanda suka yaba musu kwarai da gaske. Kusan a lokaci daya ne ake gudanar da gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da kuma gasar karshe ta wasan kwallon tennis na tsakanin mata bibbiyu. Masu sha'awar kwallon tennis ba kadan ba na kasar Sin sun yi kallon wasan tennis bisa shirin kai tsaye da aka aike ta T.V; Lallai Zhenjie da Yanzi ba su kauce wa burinsu ba,domin sun lashe 'yan wasan kasashen Spain da Argentina wato Virginia Ruano Pascual da Paola Suarez da ci biyu da daya, wato ke nan sun zama zakara a gun gasar wasan kwallon tennis na tsakanin mata bibbiyu na Wimbledon.

Muna iya fadin, cewa 'yan wasa su Zhenjie da Yanzi sun sa duniya ta kara sa ido kan wasan kwallon tennis na kasar Sin yayin da suke janyo hankulan jama'ar kasar Sin wadanda suka nuna sha'awa ga wasan kwallon tennis.


1  2  3