Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-08 16:35:00    
'Zakaru Zhenjie da Yanzi a wasan kwallon tennis na tsakanin mata bibbiyu

cri

'Yan wasa mata matasa su Zhenjie da Yanzi sun burge masu sha'awar kwallon tennis kwarai da gaske a gun gasannin wasan kwallon tennis na kasa da kasa da aka yi a wannan shekara. A cikin manyan gagaruman gasanni iri uku da aka kawo karshensu a shekarar da muke ciki, 'yan wasan su Zhenjie da Yanzi sun samu lambar zinariya a budaddiyar gasa ta wasan kwallon tennis da aka yi a kasar Australiya da kuma birnin Wimbledon na kasar Burtaniya. Wassu kwararru a fannin wasan kwallon tennis na kasar Sin sun yi hasashen, cewa ana sa ran wadannan fitattun 'yan wasa za su zama 'yan takara masu karfi dake neman karbar lambar zinariya a gun wasan kwallon tennis na tsakanin mata bibbiyu na wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing a shekarar 2008. To, yanzu bari mu dan gutsura muku wani bayani game da wadannan 'yan wasa guda biyu.

Kwanakin baya ba da dadewa ba, an gudanar da karin gasa ta kungiyar duniya ta gasar cin kofin Federation a shekarar 2006 a nan Beijing, inda 'yan wasa mata na kasar Sin suka kafa tarahi har a karo na farko ne suka shiga jerin kungiyoyi guda 8 masu karfi na kungiyar duniya na gasar cin kofin Federation. A lokacin da ake yin karawa tsakanin kungiyar kasar Sin da ta kasar Jamus, iyayen 'yan wasa wato Zhenjie da Yanzi su ma sun je filin wasan domin sa kaimi ga 'ya'yansu mata. ' Yar wasa Zhenjie ta yi farin ciki da fadin, cewa 'Lallai iyayena sun ba ni karin himma domin da ma suna so su je kasar Faransa domin kallon wasan da muka yi a gun budaddiyar gasa ta wasan kwallon tennis, amma ba su cimma burinsu ba saboda dalilin lokaci. Ina farin ciki matuka saboda sun samu damar kallon wasan a wannan gami.'


1  2  3