Babbar ganuwa tana cike da kalmade-kalmade har tsawonta ya kai fiye da kilomita 5000, ita ba wata ganuwa kawai ba, amma ta zama wani cikakken tsarin aikin yin tsaro da ke hade da gine-ginen tsaron kai daban-daban ciki har da ganuwa da tasmahara da barikokin soja da hasumiyar da aka yi da tubalai. An gina babbar ganuwa a kan manyan tsaunuka ko filayen karkara bisa halayen kasa da bukatar tsaron kai, matsakaicin tsayinta ya kai mita 7 zuwa 8, fadinta ya kai mita 6 zuwa 7 daga kasa, daga sama kuma ya kai mita 4 zuwa 5.(Umaru) 1 2 3
|