Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-07 18:21:43    
Babbar ganuwa

cri

A nan Kasar Sin da akwai wani tsohon ginin da ake kira babbar ganuwa wadda ta shakara ko'ina a duk duniya baki daya, ta hade da Shanhaiguan da ke bakin tekun Bo daga gabas, da Jiayuguwan da ke lardin Gansu daga yamma, ta ratsa manyan tsaunuka da kwaruruwa barkatai, duk tsawonta ya kai fiye da kilomita 6000, wato ta ketare larduna da biranen da ke karkashin gwamnatin tsakiya kai tsaye da kuma jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu guda 7 da ke arewacin kasar Sin.

Babbar ganuwa mai kayatarwa tana daya daga cikin manyan gine-ginen tarihin duniya. A shekarar 1987, an shigar da ita cikin "Sunayen abubuwan al'adun gargajiya na tarihin duniya". Kwamitin kula da kayayyakin tarihi na duniya ya daukaka cewa, bayan da sarki na farko na daular Qin ya hada kasar Sin da ta zama daya a shekara ta 220 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam, ya yi gyare-gyare da kuma harhada sassan gine-ginen da aka yi domin tsaron kai har suka zama wani cikakken tsarin tsaron kai wato babbar ganuwa wadda ta zama ginin soja mafi tsawo na duniya.


1  2  3