Domin kara sa kaimi ga bunkasa dagantakar da ke tsakanin Sin da Turai, cikin shekarar da ta wuce kuma kasar Sin ta kulla dangantakar aiki mai kyau a tsakaninta da kwamitin kawancen kasashen Turai, da majalisar kawancen, da majalisar Turai, da kuma kasar da ke shugabantar kawancen a wannan zagaye. Jakada Guan ya ce, "Cikin shekarar da ta wuce, shugabannin bangarorin 2 sun yi ta ganawa a tsakaninsu, alal misali, a shekarar bara, firayim ministan kasar da ke shugababantar kawancen kasashen Turai a wannan zagaye ya kawo ziyarar da ba ta aiki ba a kasar Sin, a wannan shekara kuma ya kawo ziyarar aiki a nan kasar Sin. Kuma yawancin mambobin kawancen dukkansu sun taba kawo ziyara a kasar Sin. Wannan ya ba da muhimmin taimako ga bunkasa dangantakar da ke tsakanin Sin da Turai". 1 2 3
|