Cinikin da ake yi tsakanin Sin da Turai ya zama wani muhimmin kashi ne daga cikin dangantakar da ke tsakanin bangarorin 2. Cikin shekarar da ta shige, hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da ake yi tsakanin Sin da Turai shi ma ya samu ci gaba da sauri. Jakada Guan ya bayyana cewa, "Cikin shekarar da shige, hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da ake yi tsakanin Sin da Turai ya samu ci gaba da sauri, yawan kudin da aka samu daga wannan fanni ya karu-karuwar gaske, zuwan watan Yuni na wannan shekara, yawan kudin da aka samu wajen cinikin da aka yi tsakanin Sin da Turai ya kai dala biliyan 120.9, wato ya karu da kashi 20.8 bisa 100. Yawan kudin da aka samu wajen shigo da fasaha daga kawancen kasashen Turai da kwangilolin da aka daddale a tsakanin bangarorin 2 ya kai dala biliyan 4.6, wato ya kai kusan kashi 42 cikin 100 bisa na dukkan kwangilolin da kasar Sin ta kulla domin shigo da fasaha daga kasashen waje, wato ya zarce na yawan kudin da aka samu wajen kwangilolin da aka daddale tsakanin Sin da Amurka ko Japan a wannan fanni."
1 2 3
|