Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-07 15:07:56    
Dangantakar abokantaka ta muhimman tsare-tsare da ke tsakanin Sin da Turai ta samu ci gaba cikin zama mai dorewa

cri

A ran 9 ga wata, firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin zai kai ziyara a kasar Finland, kuma zai halarci taro na 9 na shugabannin kasashen Sin da Turai da za a yi a can. A gabannin ranar bude taron, Guan Chengyuan, jakadan kasar Sin da ke wakilci a kawancen kasashen Turai ya amsa tambayoyin da manema labaru na kafofin watsa labaru na kasar Sin da ke Brussels suka yi masa ta hanyar hadin gwiwa. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku cikakken bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana game da wannan labari.

Jakada Guan Chengyuan da farko ya yi takaitaccen bayani kan ganawar da za a yi a nan gaba kadan tsakanin shugabannin kasar Sin da kasashen Turai, ya ce, "Wannan ya zama karo na 9 ke nan da za a yi shawarwari a tsakanin shugabannin kasar Sin da kasashen Turai. Ganawar da ke tsakanin su kuma ta zama wani muhimmin tsarin yin shawarwari wajen dangantakar da ke tsakanin Sin da Turai, muhimmin aikin da ake yi a gun shawarwarin shi ne domin tsara shirin bunkasa dangantakar da ke tsakanin Sin da Turai daga duk fannoni. A gun wannan ganawar da za a yi tsakanin su, za a takaita ci gaban da aka samu wajen bunkasa dangantakar da ke tsakanin Sin da Turai da wasu matsalolin da ke kasancewa a tsakanin su tun bayan shawarwari na karo na 8 da aka yi tsakanin shugabannin Sin da na kasashen Turai. Sa'an nan kuma za a nuna manufar bunkasa dangantaka a tsakanin Sin da Turai a nan gaba, da tsai da wasu muhimman manufofi, ban da wannan kuma za a yi musanyar ra'ayoyi kan matsalolin kasashen duniya da suke jawo hankulansu 2 sosai.


1  2  3