Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-06 17:44:51    
An ba da shawarar kafa kungiyar tarayyar masana'antu na kasar Sin dangane da hakkin mallakar madaba'a

cri

Masana'antu 6 da suke da nasaba da hakkin mallakar madaba'a na kasar Sin sun gabatar da shawarar kafa kungiyar tarayyar masana'antun kasar Sin da suke da nasaba da hakkin mallakar madaba'a cikin hadin guiwa bisa nacewa ga bin dokokin shari'a da ka'idoji da suke da nasaba da hakkin mallakar madaba'a na kasa da kasa da na gida. Shugaban rukunin Cartoon na San Chen Sun Wen Hua ya kirayi masana'antu da su yi hadin guiwa da gwamnati don kiyaye hakkin mallakar madaba'a, ya bayyana cewa, ya kamata a kara kyautata tsarin kiyaye hakkin mallakar ilmi, a lokacin da aka kiyaye shi, ya kamata masana'antu da gwamnati su taimaka wa juna, kuma ya kamata masana'antu su sami ra'ayi daya, wato yin takara a kasa da kasa da kuma yaki da satar hakkin mallakar madaba'a a cikin gida, sa'anan kuma bangarori daban daban suna kasancewa cikin ma'amalar juna da samun hanyoyi ba tare da kowace katanga da aka gitta musu ba da kuma taimaka wa juna a tsakaninsu da gwamnati da sauran masana'antu da hukumomin yin nazarin ilmi da kafofin watsa labaru na zamantakewar al'umma.

Mataimakin shugaban kungiyar kare hakkin mallakar ilmi ta duniya Geoffrey Yu ya bayyana cewa, shirya taron dandalin tattaunawa a wannan gami, ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali sosai ga kiyaye hakkin mallakar ilmi , wannan na da ma'ana mai muhimmanci ga raya tsarin kasar Sin na kiyaye hakkin mallakar ilmi cikin dogon lokaci , wannan kuma zai sa kaimi ga kasar Sin wajen samun ci gaba a fannonin tattalin arziki da al'adu da zamantakewar al'umma da dai sauransu. (Halima)


1  2  3