A gun taron dandalin tattaunawa, mahalatan taron sun yi bincike kan halin da masana'antun da suke da nasaba da hakkin mallakar madaba'a suke ciki da makomar samun bunkasuwa daga fannoni da yawa, kiyaye hakkin mallakar madaba'a da himmantar da kirkire-kirkire da kafa ingantaccen tsarin kiyaye hakkin mallakar madaba'a tare da samun sakamako da kuma kafa muhalli mai kyau na kiyaye hakkin mallakar madaba'a sun zama abu mai muhimmanci sosai da aka mai da hankali a kai.
Mataimakin shugaban kungiyar tarayyar manhaja ta irin kasuwanci kuma babban mai sa ido kan shiyyar Asiya da tekun Pasific Jeffrey Hardee ya bayyana cewa, bis rahoton da abin ya shafa da aka yi, an ce, idan yawan kayyayyakin da aka satar hakkinsu na mallakar manhaja a kasar Sin ya ragu da kashi 10 cikin dari, to yawan kudin shiga da kasar Sin ta samu daga wajen masana'antun IT zai kara karuwa da ninki uku bisa na yanzu a shekarar 2009, wannan ya bayyana cewa, yawan kudin da za a samu daga darajar tattalin arzikin kasar Sin zai karu da kudin Amurka dolla biliyan 87.
1 2 3
|