Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-06 17:44:51    
An ba da shawarar kafa kungiyar tarayyar masana'antu na kasar Sin dangane da hakkin mallakar madaba'a

cri

Long Xinmin

A ran 5 ga wannan wata, a nan birnin Beijing, an kita taron dandalin tattaunawa kan hakkin mallakar madaba'ar kasa da kasa na shekarar 2006, wakilai fiye da 200 da suka zo daga hukumar hakkin mallakar madaba'ar kasar Sin da hukuma mai farin jini ta kiyaye hakkin mallakar madaba'a ta kasa da kasa da shahararrun masana'antu fiye da 100 sun halarci taron don yin shawarwari kan babban shirin raya masana'antun kasar Sin da suke da nasaba da hakkin mallakar madaba'a . A gun taron dandalin tattaunawa, shahararrun masan'antun kasar Sin sun ba da shawarar kafa kungiyar tarayyar masana'antun kasar Sin kan hakkin mallakar madaba'a cikin hadin guiwa don kiyaye hakkin mallakar madaba'a ta hanyar yin amfani da karfin jama'a.

Kungiyar hakkin mallakar madaba'a ta duniya da hukumar hakkin mallakar madaba'a ta kasar Sin su ne suka shirya taron dandalin tattaunawar  cikin hadin guiwa, taron  shi ne babban taron dandalin tattaunawa mafi girma na kasa da kasa da aka shirya bisa mataki mafi girma wajen masana'antun kasar Sin da suke da nasaba da hakkin mallakar madaba'a . Shugaban babbar hukumar watsa labaru da madaba'a ta kasar Sin kuma shugaban hukumar hakkin mallakar madaba'a ta kasar Sin Long Xinmin ya bayyana cewa, bisa albarkacin kara kyautata tsarin hakkin mallakar madaba'a a kasar Sin, da kara zurfafa hadin guiwar hakkin mallakar madaba'a a tsakanin kasa da kasa, za a kara yin amfani da karfin kasuwanci da ba a taba yin amfani da shi ba wajen masana'antun da suke da nasaba da hakkin mallakar madaba'a ,makomar  na da haske sosai. Bisa tsayayyar niyyarmu da ke kara karfi ne, za mu dauki matakai masu amfani sosai don kiyayewa da sa kami ga samar da muhalli mai kyau wajen raya masana'natun da suke da nasaba da hakkin mallakar madaba'a.


1  2  3