
A karon nan na gasar rera wakoki, an kara wakokin da aka rera ta hanyar dabarun gargajiya na zamanin da da can sosai, yawancin wadanda ke shiga gasar sun zo ne daga wuraren kananan kabilu da ke nesa da birane , wakokin da suka rera na da halayen musamman na kabilunsu sosai, abubuwan da ke cikin wakoki sun shafi fannoni da yawa, kamar abubuwa dangane da zaman rayuwa da aiki da soyayya da al'adar kabilu da dai sauransu.
Wani mashahurin mai hasasshen wake-wake da kide-kide na kasar Sin Tian Qing ya bayyana cewa, a shekarar da muke ciki, an yi gasar rera wakoki ta hanyar dabarun gargajiya na zamanin da da can, wannan ya bayyana cewa, ana mai da hankali sosai ga abubuwan tarihi na gargajiya ba kayayyaki ba a zamantakiewar al'umma, duk saboda dabarun nan tushe ne na dabarun rera wakokin gargajiya na al'ummarmu. Muna da kabilu da yawansu ya kai 56 tare da makiyayar kasa da yawan fadinta ya kai murabba'in kilomita miliyan 9.6, wurare masu bambanci suna da nasu abubuwan gargajiya tare da fasahohin rera wakokinsu.
A cikin gasar, akwai mawaka guda hudu da suka rera wata waka mai suna "Xianggelila", wakar nan na da dadin ji sosai tare da nuna halin jarumtaka da kishin aiki na mutanen lardin Yunan na kasar Sin, wakar ta sami yabo sosai daga wajen 'yan kallo da masu ba da sharhi. (Halima) 1 2 3
|