Mawaka fiye da 100 sun yi amfani da dabarun rera wakoki daban daban wajen rera wakoki iri iri da yawa. Wani mawaki mai suna Xue Haoyin da ya samu lambar yabo ya bayyana cewa, a ganina, kokarin da na yi a kullum na da muhimmanci sosai wajen samun lambar yabo. Sa'anan kuma na sami lambar yabo bisa sakamakon da nake kasancewa cikin hucewar zuciya, ta hakan nan ne kwarewar rera wakoki da na yi ta bayyanu sosai.
Yawan wadanda suka shiga gasar rera wakokin gargajiya na kasar Sin a wannan karo ya kai 30 , Har sau uku ne Mr Wang Zuxian ya zama wanda mai ba da sharhi a kan wakokin da aka rera a gun irin gasar, ya bayyana dabarun da aka bi wajen rera wakoki da kuma manyan sauye-sauyen da aka samu a gun gasar wannan karon cewa, wakokin da aka rera na da dadin ji sosai, a da wakokin da aka rera yawancinsu ne na bayyana abubuwan bakin ciki da aka samu don nuna fasahohin rerawa, amma a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, an sami manyan sauye-sauye a fannin nan, an rera wakoki dangane da zaman rayuwa tare da fasahohin rerawa, na gano cewa, wakokin da aka rera a karon nan da wancan karo na da dadin ji sosai bisa na sauransu da aka yi a da.
1 2 3
|