Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-22 15:01:19    
Ko za a iya ci gaba da yin babban zaben kasar Congo Kinshasha bisa shirin da aka tsara?

cri

Amma manazarta suna ganin cewa, ko da yake har yanzu kungiyoyin da ke rike da makamai wadanda suke adawa da gwamnati da kungiyoyin adawa da gwamnati wadanda suke nuna bakin ciki ga babban zabe suna nan a kasar Congo Kinshasha, ba za a iya magance aukuwar rikice-rikice iri iri a kasar ba lokacin da ake yin babban zabe. Amma tabbas ne za a ci gaba da aiwatar da ayyukan babban zabe.

Da farko dai, jama'ar kasar Congo Kinshasha wadanda suka sha wahalolin yakin basasa kuma suke neman zaman lafiya za su zama muhimmin karfi. Tun daga shekarar 1998, mutane kusan miliyan 4 suka mutu a cikin yakin basasa. Sabo da haka, jama'ar Congo Kinshasha suna darajantar wannan babban zabe irin na dimokuradiyya na farko da ake yi a kasar bayan da kasar Congo Kinshasha ta samu 'yancin kai yau da shekaru 46 da suka wuce.

Sannan kuma, kasashen duniya suna fatan za a ci gaba da yin wannan babban zabe lami lafiya bisa shirin da aka tsara. A kwanan baya, Kofi Annan, babban sakataren M.D.D. ya bayar da jawabi, inda ya yi kira ga bangarori daban-daban da su girmama sakamakon babban zaben. Kafin a jefa kuri'a a zagayen farko na babban zabe, M.D.D. ta tura wata rundunar sojan tabbatar da zaman lafiya mai sojoji dubu 17 zuwa kasar Congo Kinshasha domin kwantar da hankali a kasar lokacin da ake yin babban zabe. Bugu da kari kuma, domin kasar Congo Kinshasha tana da wadatattun albarkatun halittu, kasashen yammacin duniya ma suna fatan za a iya kwantar da halin siyasa a kasar Congo Kinshasha. Sabo da haka, suna kuma fatan za a iya ci gaba da yin wannan babban zabe. (Sanusi Chen)


1  2  3