Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-22 15:01:19    
Ko za a iya ci gaba da yin babban zaben kasar Congo Kinshasha bisa shirin da aka tsara?

cri

Bisa kiddidigar da aka yi, a cikin zagaye na farko na babban zabe, yawan kuri'un da shugaba mai ci Mr. Kabila ya samu ya kai kashi 44.81 cikin kashi dari, amma kuri'un da malam Bemba ya samu sun kai kashi 20.03 cikin kashi dari kawai. Bayan da Mr. Kabila ya hau kan mukamin mulkin kasar Congo Kinshasha a shekara ta 2001, ya yi kokari sosai kan daidaita batutuwan da ke kasancewa a kasar ta hanyar zaman lafiya, kuma ya yi kokari sosai wajen daidaita rikice-rikicen karfin tuwo da ke kasancewa a yankunan gabashin kasar. A shekara ta 2003, Mr. Kabila ya kulla wata yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a kasar da bangarori daban-daban, ya kuma kawo karshen yakin basasa da kafa wata gwamnatin rikon kwarya wadda ke kunshe da wakilan tsohuwar gwamnati da jam'iyyun siyasa da ke adawa da gwamnati kuma da membobin kungiyoyin da ke rike da makamai da ke adawa da gwamnati. Sakamakon haka, Mr. Kabila ya samu amincewa sosai daga jama'ar yankunan gabashin kasar domin kokarin kwantar da hankali a yankunan da ya bayar. Sabo da haka, yawancin mabiyansa sun fito daga yankunan gabashin kasar inda ke da arzikin albarkatun halittu da mutane.

Amma Mataimakinsa, Mr. Jean Pierre Bemba, tsohon jagoran kungiyar da ke rike da makamai wadda ke adawa da gwamnati. Yawancin mabiyansa sun fito ne daga yankunan yammacin kasar ciki har da birnin Kinshasha, hedkwatar kasar.

Wani babban hafsan rundunar soja ta gwamnatin Congo Kinshasha wanda ba ya son bayar da sunansa a fili, ya ce, yanzu dakarun tsaron lafiyar shugaba Kabila suna mallakar halin da ake ciki a kasar, kuma suna farautar dakarun tsaron lafiyar Bemba.


1  2  3