Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-22 15:01:19    
Ko za a iya ci gaba da yin babban zaben kasar Congo Kinshasha bisa shirin da aka tsara?

cri

A ran 21 ga wata, dakarun tsaron lafiyar shugaba Josef Kabila da dakarun tsaron lafiyar Jean Pierre Bemba, mataimakin shugaban kasar Congo Kinshasha sun sake yin fada da juna sosai a birnin Kinshasha. Bisa sakamakon da kwamitin kula da harkokin zabe mai 'yanci na kasar ya bayar, an ce, babu wani dan takara da ya samu kuri'u fiye da kashi 50 cikin kashi dari a gun zagaye na farko na babban zaben da aka yi a karshen watan Yuli. Sakamakon haka, Mr. Kabila da Mr. Bemba wadanda suke gaba kan dukkan 'yan takara za su shiga zagaye na biyu domin neman mukamin shugaban kasar. Amma yanzu ana nuna damuwa sosai shin ko za a iya yin zagaye na biyu na babban zabe a kasar bisa shirin da aka tsara bayan da aka ta da rikicin karfin tuwo a tsakanin dakarun tsaron lafiyarsu?

Dakarun tsaron lafiyar wadannan 'yan takara 2 sun fara yin fada da juna ne a ran 20 ga wata da dare, abin da ya yi sanaddiyar mutuwar mutane a kalla 5 tare da ji wa mutane 5 raunuka. Lokacin da suke fada da juna, kwamitin kula da harkokin zabe mai 'yanci na kasar ya bayar da sakamakon zagaye na farko na babban zabe ga jama'a.


1  2  3