Wani shugaban da abin ya shafa na hukumar sa ido da kula da harkoki kan abinci da magungunan sha ta kasar Sin Zhang Wei ya bayyana cewa, kodayake an riga an kammala gwaji na matakin farko, amma ba a nufi cewa, masu yin nazari da binciken kimiyya na kasar Sin za su iya ci gaba da gwajin binciken allurar nan nan da nan, ya ce, yanzu, masu binciken kimiya kan aikin nan suna nan suna yin bincike kan sakamakon da aka samu wajen yin gwajin matakin farko a asibiti , ko za su ci gaba da gwajin nan, ba a yanke shawara ba sai bayan da kwararru su yi bincike da kimantawa a kan sakamakon daga dukan fannoni.
Mr Zhang Wei ya ce, ana bukatar yin gwaje-gwaje a cikin sauran matakai biyu a kan allurar, don ci gaba da dudduba ingancin allurar nan wajen yin afmani da ita da kuma dudduba a kan yadda allurar nan za ta kare lafiyar wadanda suka kamu da ciwon sida . ba za a iya yin amfani da allurar nan da kera ta ba sai ta sami izni bayan gwaje-gwajen da aka yi a matakai uku a asibiti.
Ya zuwa yanzu, an riga an yi gwajin allurar rigakafin ciwon sida da yawansu ya kai 120 a asibiti a duk duniya, yawancinsu ne suke kasancewa cikin matakin farko .
Mataimakin ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Liu Yanhua ya bayyana cewa, wajen binciken allurar rigakafin ciwon sida, kasar Sin tana son bin ka'idojin kasa da kasa da kuma yin hadin guiwa da kasa da kasa, ta yadda sakamakon da ta samu zai iya ba da gudumuwa ga bunkasuwar kasar Sin da duk dunya.(Halima) 1 2 3
|