Yanzu, kasar Sin ta riga ta kammala gwajin yin amfani da allurar farko ta yin rigakafin maganin ciwon sida a matakin farko a asibiti, wani jami'in kasar Sin ya bayyana cewa, sakamakon farko da aka samu ya bayyana cewa, irin allurar nan na da lafiya wajen yin amfani da ita, kuma ta iya sa mutum ya sami karfin garkuwar jiki wajen maganin kwayoyin cutar sida.
Bisa kididdigar da hukumar tsara shiri kan ciwon sida ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi, an ce, tun daga shekarar 1981 da kasar Amurka ta yi shelar samun wanda ya kamu da ciwon sida a karo na farko a duniya har zuwa yanzu, yawan wadanda suka mutu bisa sanadiyar kamuwa da ciwon sida ya riga ya kai miliyan 25 a duk duniya. Yanzu, kwararru na kasashe daban daban suna ganin cewa, yin nazari da kuma kera allurar rigakafin ciwon sida babbar hanya ce ta yi nasarar maganin ciwon nan. Saboda haka kasashe daban daban suna nan suna kara yunkurinsu wajen yin nazari da kera allurar rigakafin ciwon, kasar Sin ita ma tana cikinsu.
1 2 3
|