Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-21 17:16:17    
Kasar Sin ta kammala gwajin yin amfani da allurar farko ta yin rigakafin maganin ciwon sida a matakin farko a asibiti

cri

Tun daga shekarar 1996 har zuwa yanzu, masu binciken kimiyya na kasar Sin sun yi ayyukan bincike da yawa a kan kwayoyin cutar sida wadanda suke yaduwa a kasar Sin , a karshe dai sun sami wata allurar rigakafin ciwon sida, kuma tun daga watan Maris na shekarar bara, sun soma yin nazarin bincike na matakin farko a kan irin allurar a asibiti don dudduba ingancinta.

Shahu malami mai kula da aikin yin nazari da bincike kan allurar nan Kong Wei ya bayyana cewa, gwajin da suka yi yana bin ajandojin kasa da kasa sosai da sosai, a cikin shekarar bara, an sa allurar nan ga masu sa kai da yawansu ya kai 49 a kai a kai, sa'anan kuma aka dudduba lafiyar jikinsu da kuma yi musu gwajin bincike ba tare da rabuwar da su ba a cikin kwanaki 180.

Malam San Guowei, shugaban hukumar bincike da tabbatar da magungunan sha da aka yi da kayayyakin halittu na hukumar sa ido da kula da harkoki kan abinci da magungunan sha ta kasar Sin ya bayyana cewa, sakamakon da aka samu wajen gwajin nan ya bayyana cewa, allurar nan na da lafiya wajen maganin ciwon sida. Ya ce, daga wajen sakamakon da aka samu a gun gwajin da aka yi, ana iya ganin cewa, ba a sami cikas mai tsanani a wani kashin jiki ko duk jikin mutum ba, amma wasu wadanda aka sa musu allurar sun riga sun sami karfin garkuwar jiki wajen maganin kwayoyin cutar sida da sauransu.


1  2  3