
Zaman lafiya da bunkasuwa sun zama manyan batutuwa 2 na duniyar yanzu. Bisa matsayinsu na kasashe masu bunkasuwa, kasar Sin da kasashen Afirka dukkansu suna fuskantar ayyukan tarayya na bunkasa tattalin arzikin al'umma da daga matsayin zaman rayuwar jama'a. Domin nuna goyon baya ga matan kasashen Afirka don su samun ci gaba da bunkasuwa, da taimaka wa kungiyoyin mata na kasashe daban-daban na Afirka, hadaddiyar kungiyar mata ta kasar Sin ta ba da gudummuwa gwargwadon karfinta ga kungiyoyin mata na Afirka wajen kayayyaki da fasaha a kowace shekara kuma ba tare da kowane sharadi ba.
Yanzu hadaddiyar kungiyar mata ta kasar Sin ta riga ta kafa dangantaka a tsakaninta da kungiyoyin mata fiye da 100 na kasashe 46 na Afirka, bisa saurin ci gaban dangantakar abokantaka irin na sabon salo na muhimman tsare-tsare tsakanin kasar Sin da Afirka, zirga-zirgar da ke ake yi tsakanin matan kasar Sin da na Afirka suna ta karuwa a kowace rana, wannan yana da amfani ga kara jawo tasirin kasar Sin ga kasashen Afirka, da kara inganta da karfafa zumunci a tsakanin jama'ar Sin da ta Afirka. 1 2 3
|