
Sai dai kuma wani abun lura shi ne, bayan da kasar Sin ta fara tafiyar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, zirga-zirgar da matan kasar Sin ke yi tsakanin kasa da kasa su ma sun karu da sauri, haka ma tsakanin matan kasar Sin da na Afirka. A shekarar 1995 a nan birnin Beijing ne aka bude babban taron matan duniya na 4 na M.D.D. "Sanarwar Beijing" da "tsarin ka'dojin aiki" da aka bayar a gun taron sun jawo babban tasiri ga kasashe daban- daban ciki har da kasashen Afirka. A shekarar 2000, kasar Sin da kasashen Afirka sun ba da shawara tare domin kafa dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wannan kuma ya gabatar da dandalin yin hakikanan abubuwa cikin hadin gwiwa tsakanin matan kasar Sin da na Afirka.
1 2 3
|