Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-11 15:47:26    
Matan kasar Sin da na Afirka 'yanuwa ne na kusan jini daya

cri

Zirga-zirgar da ake yi tsakanin matan kasar Sin da na Afirka ya zama wani kashi da ba za a iya watsi da shi ba cikin harkokin waje da kasar Sin ke tafiyar da su kan kasashen Afirka, tun rabin karnin da ya wuce na bayan da aka kafa huldar jakadanci tsakanin sabuwar kasar Sin da kasashen Afirka, dangantakar da ke tsakanin matan kasar Sin da na Afirka ta samu bunkasuwa daga abokan sadaukantaka wajen yin adawa da masu nuna isa da 'yan mulkin mallaka zuwa 'yanuwa na kusan jini daya, sun samu manyan nasarori masu faranta ran jama'a na bangarori 2. Musamman ma bisa sabon halin da ake ciki yanzu, zirga-zirgar da ake yi tsakanin matan kasar Sin da na Afirka sun samu bunkasuwa daga fannoni daban-daban. A ran 10 ga wata, jaridar "People's Daily" ta buga wani bayanin da madam Long Jiangwen, mataimakiyar shugaban hukumar kasashen duniya ta hadaddiyar kungiyar mata ta kasar Sin ta rubuta wanda a ciki ta bayyana kyakkyawar dangantaka a tsakanin matan kasar Sin da na Afirka. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku takaitaccen bayanin.

Akwai wani karin magana na kasar Sin cewa, "A kusa ko a nesa, mu abokan juna ne." Ko da yake akwai babban nisa a tsakanin kasar Sin da Afirka, amma huldar yin mu'amalar juna a tsakanin matan kasar Sin da na Afirka tana da daddaden tarihi. Tun a watan Yuli na shekarar 1954 ma sai hadaddiyar kungiyar mata ta kasar Sin ta gayyaci kungiyar wakilan mata ta Jam'iyyar ANC ta Afirka ta kudu zuwan nan kasar Sin don yin ziyara, wannan ya bayyana babban goyon bayan da matan kasar Sin suke nuna wa tarin matan Afirka wajen famarsu ta neman samun 'yan al'umma.


1  2  3