Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-11 15:39:53    
Masana'antun dabi'i na kasar Sin sun yi albarka

cri

Wannan babbar giwa kuwa ta nuna karfinta sosai da zarar ta shiga kasuwanni. Ya zuwa yanzu dai, rukunin kamfunna buga littattafai na kasar Sin ya riga ya sami mallakar sama da kashi 7% na kasuwannin littattafai na kasar Sin.

Daidai kamar yadda rukunin kamfunna buga littattafai na kasar Sin ya yi, sakamakon gyare-gyaren, sabbin masana'antun buga littattafai masu yawa na kasar Sin sun fara nuna karfinsu a cikin kasuwanni.

Ban da kasuwannin gida, wadannan sabbin masana'antun buga littattafai na kasar Sin sun kuma aiwatar da manufar 'fita waje', sun yi kokarin shiga takarar da ke tsakanin kasashen duniya baki daya. Bikin baje koli na littattafai na Frankfort wanda a kan shirya a shekara shekara bikin baje koli ne mafi girma na littattafai a halin yanzu a duk duniya. Kusan kashi 75% na cinikin hakkin mallakar littattafai na duk duniya an kulla ne a nan wurin, sabo da haka, wannan bikin baje koli ya zama tamkar wani dandali na yin bincike a kan masana'antun buga littattafai na kasashe daban daban. Amma a gun bikin na da, yawan hakkin mallakar littattafai da kasar Sin ta shigo ya kan ninka wa hakkin nan da ta fitar har sau goma ko kuma fiye, tana tsananin rashin samun daidaici a tsakanin shigowa da fitarwa da hakkin mallakar littattafai. Amma a wannan shekara, yawan hakkin mallakar littattafai da kasar Sin ta shigo ya kai 881 a yayin da yawan hakkin nan da ta fitar ya kai 615, wato ta rage gibin da ya kasance a wannan fanni kwarai da gaske ke nan, kuma ta kara yawan littattafanta a kasuwannin duniya. Shugaban sashen kula da manufofi na babbar hukumar kula da harkokin buga littattafai ta kasar Sin, Mr.Wang Tao ya bayyana cewa, 'wannan abin farin ciki ne da ba a same shi har shekaru da dama ba. Me ya kawo wannan sauyi kuma? Kara karfi da masana'antun buga littattafai suka yi sakamakon gyare-gyare shi ya kawo wannan sauyi. A wajen cinikin hakkin mallakar littattafai, idan ba ka da karfin kirkirowa, amma kana son sayar da kayanka, to, za a ki saya. Wannan sauyi mai farin jini da aka samu a wajen cinikin hakkin mallakar littattafai ya nuna cewa, karfin masana'antun buga littattafai na kasar Sin ya karu sakamakon gyare-gyare.' (Lubabatu Lei)


1  2  3