Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-11 15:39:53    
Masana'antun dabi'i na kasar Sin sun yi albarka

cri

Yau idan ka zagaya a kantunan sai da littattafai na kasar Sin, to, za ka tarar da cewa, ire-iren littattafan da ake bugawa a nan kasar Sin sai kara yawa suke yi. Wadannan littattafai dai sun shafi al'adu da tarihi da zaman al'umma da kimiyya da fasaha da zaman rayuwa da wasa kwakwalwa da dai sauran fannoni baki daya, sai ka ce babu abin da aka rasa. Kasuwannin littattafai na kasar Sin sun yi albarka kwarai da gakse. Babban kantin sai da littattafai nan birnin Beijing, wani babban kanti ne na kasar Sin wanda ke sayar da littattafai iri iri. A ko wace rana, da zarar aka bude kofar kantin, sai masu saya sun yi ta shigowa ba tare da tsayawa ba. A sa'in da jama'a suke sayan littattfai a nan, suna kuma ganewa idonsu kan irin sauye-sauyen da ake samu a kasuwar littattafai.

Madam Li Fen, wadda ta kasa zabar littafin da za ta saya sabo da littattafai iri daban daban masu matukar yawa da ke cikin wannan kanti. Ta ce, 'yanzu akwai littattafai iri iri masu yawa, ana iya sayen littafi na ko wane iri idan an je babban kantin.'


1  2  3