Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-11 15:39:53    
Masana'antun dabi'i na kasar Sin sun yi albarka

cri

A cikin 'yan shekarun nan, yawan littattafan da ake sayarwa a cikin babban kantin sai da littattafai na Beijing yana dinga karuwa bisa kashi 20% a ko wace shekara. A shekarar bara, yawan kudin da kantin nan ya samu daga sai da littattafai ya kai har kudin Sin yuan miliyan 440. Bisa kidayar da aka yi, an ce, a shekara ta 2005, gaba daya ne kasar Sin ta buga littattafai wadanda ire-irensu suka kai sama da dubu 220, adadin nan ya kuma karu da kusan kashi 8% bisa na shekarar da ta gabata, wanda kuma ya ninka har sau 10 bisa na shekara ta 1978.

Irin wannan albarka da aka samu a cikin kasuwar littattafai ya bambanta kwarai da gaske da halin da kantunan sai da littattafai na wurare daban daban na kasar Sin ke ciki a shekarun 1980 zuwa na 1990. A lokacin, yawancin kamfunnan buga littattafai na kasar Sin masana'antu ne na gwamnati wadanda ba don neman cin riba ne suke buga littattafai ba, sabo da haka, sun dade suna rabuwa da kasuwanni, littattafan da suka bayar ma da kyar suke biyan bukatun masu karatu.

Don neman bunkasa tattalin arziki na kasuwanni. Tun daga karshen karnin da ya gabata, kasar Sin ta fara aiwatar da gyare-gyare a fannin masana'antun buga littattafai don su biya bukatun kasuwanni. Sakamakon gyare-gyaren, bi da bi ne masana'antun buga littattafai na kasar Sin sun sauya tsarinsu, masana'antu masu yawa da suka samu karfin takara a kasuwanni sun fito. A shekara ta 2002, rukunin kamfunnan buga littattafai na kasar Sin, wato kamfunnan buga littattafai mafi girma na kasar Sin wadda ke kunshe da masana'antu fiye da 10 ya kafu. Yayin da yake bayyana dalilin da ya sa aka kafa wannan rukuni, babban darektan rukunin, Yang Muzhi ya ce, 'makasudin kafa wannan rukuni shi ne farfado da tsarinmu, a yi gyare-gyare, don kafa wani sabon rukuni mai karfi. Za mu shafe shekaru 3 zuwa 5 muna kokari, ta yadda kamfaninmu zai zama wata babbar giwa a tsakanin masana'antun buga littattafai.


1  2  3