Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-09 17:02:38    
Wani mashahurin likita na zamanin da na kasar Sin mai suna Li Shizhen

cri

Li Shizhen ya kara kwarewa, kuma ya yi suna sosai a tsakanin jama'a, a wancan zamani , mutanen da suke zama a fadar sarki su ma sun gayyace shi don shawo kan ciwace-ciwacen da suke kamuwa da su, kuma Li Shizhen ya yi nasarar warkar da ciwace-ciwace wadanda da kyar ake iya warkar da su, bisa sakamakon nan ne sarki ya nada shi don ya zama jami'in kula da harkokin likitanci, kodayake Li Shizhen ya yi aiki a fadar sarki, amma ya kan fita waje don dudduba lafiyar mutanen da suka yi zama kamar da kowa. A lokacin da yake duba marasa lafiya, Li Shizhen ya kan yi kokarin nazarin shahararren littattafan likitanci, a kai a kai ne ya gano wasu kurakurai a cikin littattafan, sai ya gyara su ta hanyar aikatawarsa na hakika.

A duk rayuwarsa, Li Shizhen ya rubuta littattafan likitanci da yawa, a karshen rayuwarsa, ya kammala rubuta wani mashahurin littafi da ke da lakabi haka: Compendium of materia medica. Littafin nan yana da babi da yawansu ya kai 52 tare da rubuta abubuwa dangane da ire-iren magunguna da yawansu ya kai 1892 , daga cikinsu, yawan ire-iren tsire-tsire ya kai 1195 da na ire-iren dabbobi 357 da na ma'adinai 357. sa'anan kuma a cikin littafin, ya rubuta abubuwa dangane da shirye-shiryen ba da magani da yawansu ya kai 11096 da yawan zane-zanen da ya yi dangane da ire-iren duwatsu da tsire-tsire ya kai 1160. Littafin nan ya bayyana inda aka sami tsire-tsiren magunguna iri daban daban da sifofinsu da yadda ake dasa su da nomansu da cire su da kuma bayyana halin musamman na magungunan da amfaninsu. Wata gudumowa mai muhimmanci da Li Shizhen ya bayar shi ne gyara kurakurai da yawa da mutanen da suka zo kafinsa suka yi ta hanyar kimiyya. Sa'anan kuma ya sami wani sakamako mafi muhimmanci wajen harhada magunguna da yanayin kasa da yanayin sararin samaniya da dai sauransu.(Halima)


1  2  3