Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-09 17:02:38    
Wani mashahurin likita na zamanin da na kasar Sin mai suna Li Shizhen

cri

Ilmin likitancin kasar Sin yana da dogon tarihi. A gun tarihin yin likitanci da harhada magunguna da ke da shekaru dubai, kasar Sin ta samu shahararrun likitoci mafiya yawa. Yau za mu bayyana wani likita na kasar Sin da ya yi zaman rayuwa a karni na 16 wanda duk duniya ta amince da shi da cewar shahararen dan kimiyya ne wajen ilmin halitta.

An haifi Li Shizhen a shekarar 1518 a lardin Hubei da ke kudancin kasar Sin. Garinsa na da ni'ima sosai, kuma ya fitar da magungunan da aka yi da tsire-tsire iri iri da yawa. Kakansa da mahaifinsa dukansu likitoci ne. tun lokacin da ya ke karami, mahaifinsa ya kan hawan tsaunuka don cire tsire-tsiren magunguna tare da shi , kuma ya bayyana masa ilmi iri iri dangane da magungunan gargajiyar kasar Sin , a kai a kai ne Mr Li Shizhen ya nuna sha'awa sosai ga magungunan gargajiyar kasar Sin . amma mahaifinsa bai amince da sha'awarsa wajen koyon ilmin likitanci ba duk saboda matsayin likitanci kasa kasa ne a zamanin gargajiyar mulki na kasar Sin, burin mahaifinsa shi ne , ya kamata ya zama jami'in gwamnati ta hanyar jarrabawa.


1  2  3