Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-08 20:04:54    
Ana tafiyar aikin shirya wasannin Olimpic lami lafiya

cri

Dayake yau rana ce da ta rage shekaru biyu da za a yi bikin bude wasannin Olimpic na birnin Beijing, shi ya sa mutane sun mai da hankulansu ga yau da shekaru biyu masu zuwa. Wasu mutane suna damuwa cewa, a yanayin rani, ana yawan ruwan sama a nan birnin Beijing, in za a sami guguwar iska tare da ruwan sama kamar da bakin kwarya, to ba abu mai kyau ba ne ga gasannin da za a yi, amma kwamitin shirya wasannin Olimpic na Beijing ya bayyana cewa, za a iya kaucewar mummunan yanayin sararin samaniya a lokacin yin gasannin wasanni da bikin bude wasannin.

A gun taron bayar da labarai, mataimakin shugaban kwamitin shirya wasannin Olimpic na Beijing Jaing xiaoyu ya bayyana cewa, mun riga mun yi nazari kan ajiyayyun takardu dangane da yanayin sararin samaniya na birnin Beijing, za a iya bayyana cewa, lokacin nan zai iya dacewa da bukatun wasannin Olimpic na shekarar 2008 a fannin yanayin sararin samaniya, sassan da abin ya shafa su ma sun yi nazari don daukar matakai iri iri don rage mummunan tasirin da yanayin sararin samaniya zai kawo.


1  2  3