Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-08 20:04:54    
Ana tafiyar aikin shirya wasannin Olimpic lami lafiya

cri

Ran 8 ga watan Augusta rana ce ta sauran shekaru biyu da yin wasannin Olimpic na shekarar 2008, a wannan rana a nan birnin Beijing, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya kira taron bayar da labarai, inda aka gayyaci manyan jami'ai na kwamitin shirya wasannin Olimpic na birnin Beijing da su bayyana halin da ake ciki wajenshirya wasannin Olimpic na shekarar 2008. Manyan jami'ai na kwamitin shriya wasannin Olimpic na birnin Beijing sun bayyana cewa, ayyuka daban daban na wasannin Olimpic da ake yi suna nan suna tafiya bis shirin d aka tsara lami lafiya.

A gun taron bayar da labarai, mataimakin shugaba kuma babban magatakarda na kwamaitin shirya wasannin Olimpic na Beijing Wang Wei ya bayyana cewa, a cikin shekaru biyar da suka wuce ko fiye da ake shirya wasannin Olimpic na Beijing, ayyuka daban daban suna nan suna tafiya lami lafiya. Tun daga karshen shekarar 2003 ne, aka soma ayyukan gina sabbin dakuna da filaye na yin gasannin wasannin Olimpic daya bayan daya, fasalolin gine-gine da aka tsara suna nan suna zama na hakika. An kuma kammala yin shirye-shiryen ranakun yin gasannin wasannin Olimpic na Beijing da yawansu ya kai 38 tare da kananan gasannin da yawansu ya kai 301. Daga watan Augusta ma shekarar 2006 zuwa yanayin bazara na shekarar 2008, a kai a kai ne za a yi gasannin share fage har sau 40, sakamakon da aka samu wajen kasuwannin tattara kudade domin shirya wasannin Olimpic na da kyau sosai, kuma za a iya kawo fatan alheri ga makomar wasannin Olimpic kuma za a iya biyan bukatun da aka yi wajen wasannin Olimpic. An riga an samu masana'antu fiye da 30 na gida da na waje da suka zama 'yan kasuwa masu ba da kyautar taimako bisa matsayi daban daban , sa'anan kuma wasannin Olimpic na nakasassu ana shirya su a daidai lokacin, kuma na bayar da tambarin wasannin Olimpic na nakasassu, ana nan ana kara saurin gine-ginen da ba su da katangar da aka gitta, kuma an soma shirin kafa kasuwannin wasannin Olimpic na nakasassu , a watan Saptumba na shekarar da muke ciki, za a bayar da alamar nuna alheri na wasannin Olimpic na nakasassu , daga dukan fannoni ne ake soma ayyukan ba da hidima ga wasannin Olimpic da suka hada da zirga-zirga da tsaron lafiya da wuraren kwana da abinci da likitanci da dai sauransu, hotel-hotel fiye da 100 tare da asibitoci 21 za su ba da hidima ga masu yawon shakatawa na gida da na waje wajen kwana da likitanci.


1  2  3