
Yanzu ana mai da hankali sosai kan ayyukan shiri na wasannin Olympis na shekarar 2008. Ga misali, akwai mutane masu yawon shakatawa kamar miliyan 1.5 za su shiga birnin Beijing a lokacin yin wasannin, ko za a iya daidaita maganar cunkuso a nan birnin Beijing? Game da wannan tambaya, Mr. Liu Qi ya ce, Beijing ya riga ya fito da shirin daidaitawa. "Da farko, za mu kara gina manyan ayyuka na tafiye-tafiye, kamar jiragen kasa da ke tafiya a karkashin kasa da muke ginawa yanzu, kuma kafa tsarin bus mai sauri. Na biyu, sarrafa da tafiye-tafiye na dan lokaci, ta haka don tabbatar da tafiye-tafiyen wasannin."
Ban da haka kuma, Beijing yana yin kokari don cika al'kawarinsa na shirya wasannin "Olympic mai kore-shar". Mr. Liu Qi ya bayyana cewa, sau na farko kasar Sin ta jagora wasannin Olympic bisa matsayin kasa mai tasowa, ba ta da ilmi sosai a fannoni dabam dabam, kuma za ta fuskanci ayyuka da yawa a cikin shekaru biyu masu zuwa, amma ya amince da cewa, kokarin da ake yi zai tabbatar da wani taron wasanin Olympic mai kyau a shekarar 2008.
Olympic yana da babbar ma'ana ta musamman ga kasar Sin, Mr. LiuQi ya ce, Da farko, wannan mafarki da kabilun kasar Sin suka yi kafin shekaru dari, a shekarar 1908 an taba yi tambayoyi uku a kan wata jarida cewa, yaushe kasar Sin za ta shiga wasannin Olympic? Yaushe kasar Sin za ta sami lambar zinariya? Yaushe kasar Sin za ta karbi bakuncin wasannin Olympic? Yanzu, muna da duk amsoshi uku. Na biyu, wasannin Olympic zai nuna al'adun kasar Sin na shekaru dubu 5 da suka wuce da sakamakon da kasar Sin ta samu kan bunkasuwar zamani. Game da kasar Sin, Wasannin Olympic zai kara amincin da ke tsakaninta da kasashen duniya, kuma ya zama wata hanya ce don nuna manufar 'duniya daya, mafarki daya'." 1 2 3
|