
Yanzu lokaci ya yi da za mu gabatar muku da shirinmu na mu leka kasar Sin. A cikin shirinmu na yau za mu karanta muku wani bayani bayan da aka kai ziyara ga Mr LiuQi, shugaban kwamitin shirin wasannin Olympic na Beijing (wato BOCOG). Bayanin yana da kanun labari cewa, Ana yin ayyukan shirin wasannin Olympic na Beijing lami lafiya har shekaru 5.
A cikin shekaru 5 tun daga bayan kwamitin wasannin Olympic na kasashen duniya ya ba da labari cewa za a bude wasannin Olympic na shekarar 2008 a birnin Beijing, kullum kasashen duniya suna mai da hankulansu kan cigaban ayyukan shirin wasannin. A kwanakin baya, Mr. Liu Qi shugaban kwamitin shirin wasannin Olympic na Beijing ya ce, ana tafiyar da ayyukan shirin ba tare da matsala ba, kuma an samu cigaban da ake so a cikin sheakaru 5 da suka wuce. Wannan ya kafa tushe mai tabbaici wajen yin wani taron wasannin Olympic mai kyau.
1 2 3
|