Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-07 21:09:33    
Ana yin ayyukan shirin wasannin Olympic na Beijing lami lafiya har shekaru 5

cri

Liu Qi

Bisa gabatarwar da Mr. Liu Qi ya yi, da kyar kwamitin wasannin Olympic na kasashen duniya ya baiwa birnin Beijing ikon jagorancin wasannin, an fara yin ayyukan shiri. Tun daga karshen shekarar 2003, aka fara gina sabbin filayen motsa jiki bi da bi. An riga an tsai da lokacin duk gasannin da za a yi. Tun daga watan Agusta na shekarar 2006 zuwan bazarar shekarar 2008, za a yi gasannin jarabawa kusan sau 40 a jere. Ban da haka kuma an zuba cikakken jari don yin wannan wasannin Olympic, akwai kamfannoni fiye da 30 daga gida ko waje sun zama 'yan kasuwa masu ba da taimako. A sa'i daya kuma ana tafiyar da ayyukan shirin taron wasannin Olympic na nakasassu, yanzu an riga an kaddamar da tambarin taron wasannin, kuma ana gina manyan ayyukan maras shinge. Kuma an riga an fara tafiyar da ayyukan zirga-zirga, tsaro, masauki, abinci, da kiwon lafiya a duk fannoni, hotel fiye da 100 da asibitoci 21 da za su yi wa masu yawon shakatawa daga gida da na waje hidima.

Mr. LiuQi ya nuna cewa, tun daga neman ikon karba bakuncin wasannin zuwa tafiyar da ayyukan shiri cikin ami lafiya, abin mafi muhimmanci shi ne kwamitin BOCOG ya samu goyon baya na gwamnatin kasar Sin da na mutane daga fannoni dabam daban, gwamnatin tsakiya ta ba da manufofin da le dace da ayyukan, kuma mutane suna ba da taimako cikin himma da kwazo. Ya ce, "Ayyukan shiri ya samun goyon bayan jama'a sosai, a cikin ayyukain zabi tambarin taro, kayyaki masu sa'a, take da wakoki na wasannin Olympic, abokai da yawa sun aiko da ayyukansu, a cikin wadannan ayyuka, mun gamu da kyyakyawan fata daga mutunen ko ina a duniya."

Tun daga an fara neman ikon yin wasannin, Beijing ya bayar da manufar "sabon Beijing, sabon Olympic", wato kara bunkasuwar zamanni na birnin Beijing ta hanyar yin wasannin Olympic.


1  2  3