Ya zuwa yanzu dai, Tangshan ya riga ya zama daya daga cikin manyan biranen kasar Sin. Mr.Zhang ya ce, a cikin shekaru 30 da suka wuce, birnin Tangshan ya mai da muhimmanci a kan aikin ba da ilmi da al'adu da kiwon lafiya da dai sauran harkokin zaman al'umma, kuma an biya bukatun jama'a a fannin al'adu da lafiyar jiki kamar yadda ya kamata. 'mun sa kaimi ga bunkasuwar harkokin zaman al'umma daban daban daga dukan fannoni, an kara saurin ci gaban kimiyya, aikin ba da ilmi ma yana bunkasa da sauri, ayyukan al'adu sun yi albarka, aikin kiwon lafiya ma ya inganta kwarai da gaske. An kyautata zaman rayuwar jama'ar Tangshan sosai.
Mr.Li Liancheng, wani mazauni birnin Tangshan, wanda ya gane wa idonsa saurin bunkasuwar Tangshan a cikin shekaru 30 da suka wuce, kuma shi da kansa ne ya ji yadda aka kyautata zaman rayuwar jama'ar Tangshan. 'Tangshan na yanzu ya fi na da. A da, babu gine-gine masu yawa a birninmu, wadannan gine-gine dukansu sababbi ne da aka gina bayan girgizar kasa. A lokacin da aka yi girgizar kasa, muna cikin mawuyacin hali, amma ga shi yanzu, ba mu rasa kome ba, gidanmu ma ya fi na da girma.'(Lubabatu Lei) 1 2 3
|