Bayan aukuwar girgizar, sai nan da nan gwamnatin kasar Sin ta kafa hukumar ba da jagoranci, don ba da jagoranci a kan ayyuka daban daban na tinkarar girgizar da kuma ba da agaji, kuma ta sai kaimi ga jama'ar bangarori daban daban na kasar da su ba da taimako ga Tangshan. A cikin shekaru da dama bayan girgizar, gwamnatin kasar Sin ta kuma aiwatar da ayyuka na farfado da Tangshan.
Wannan babbar girgizar kasa da ta auku a Tangshan ta taba firgita duk duniya, ga shi yau shekaru 30 sun wuce, tasowar Tangshan da kuma bunkasuwarta cikin sauri sun sake jawo hankulan duniya. A gun taron, Mr.Zhang ya yi bayani a kan bunkasuwar birnin Tangshan a cikin shekaru 30 da suka wuce. Ya ce. 'A cikin farkon shekaru 10 bayan girgizar, birnin Tangshan ya sami babbar nasara a wajen yaki da girgizar kasa. Sa'an nan a cikin shekaru goma na biyu, an farfado da tattalin arzikin birnin Tangshan daga dukan fannoni. A cikin shekaru 10 na uku kuma, birnin Tangshan ya shiga wani sabon mataki na samun dawammamiyar bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma cikin sauri kuma lami lafiya.'
Mr.Zhang ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun baya, a zahiri dai, birnin Tangshan ya kara karfin inganta manyan ayyuka da kayayyakin amfanin jama'a da kuma aikin gina gidaje, ya kuma bayar da makuden kudade da 'yan kwadago a wajen samar da wutar lantarki da ruwa da kula da kazamin ruwa da dai sauransu. A shekara ta 1990, birnin Tangshan ya kuma sami lambar yabo ta muhallin zaman jama'a mai kyau daga wajen MDD. A sa'i daya kuma, birnin Tangshan ya kara saurin bunkasa ayyukan noma, ya kuma sa kaimi da a bunkasa masana'antu masu fasahar zamani. Ban da wannan, Tangshan ya kuma kara bude kofarta ga kasashen waje, ya yi ta jawo jarin waje. A halin yanzu dai, akwai 'yan kasuwa daga kasashe da shiyyoyi sama da 40 na duk duniya da suka zo Tangshan don zuba jari da kuma kafa masana'antu.
1 2 3
|