Yau Jumma'a ranar 28 ga wata, rana ce ta cikon shekaru 30 da aka yi girgizar kasa a birnin Tangshan na kasar Sin, a ran nan, an yi jerin bukukuwa a birnin Tangshan don tunawa da yaki da girgizar. A gun taron da aka yi a wannan rana don tunawa da cikon shekaru 30 da aka yaki da girgizar kasa, sakataren kwamitin jam'iyyar kwaminis ta birnin Tangshan, Mr.Zhang He ya ce, a cikin shekaru 30 da suka wuce, birnin Tangshan ya sami manyan sauye-sauye a fannonin manyan ayyuka da ilmi da al'adu da kiwon lafiya da dai sauransu, kuma an yi ta kyautata zaman rayuwar mazaunan birnin sama da miliyan 7.
A ran 28 ga watan Yuli na shekara ta 1976, an yi girgizar kasa da karfinta ya kai digiri 7.8 bisa ma'aunin Richter a birnin Tangshan na lardin Hebei da ke arewacin kasar Sin. sakamakon girgizar, mutane fiye da dubu 240 sun mutu, a yayin da wasu sama da dubu 160 sun ji raunuka, kuma birnin Tangshan ya zama kufayi.
1 2 3
|